An fara sukar Amurka a kan Syria

Hakkin mallakar hoto AP

Sama da jami'an harkokin wajen Amurka 50 ne suka ratttaba hannu a kan wata takarda, suna sukar manufofin gwamnatin Barak Obama a kan kasar Syria.

Takardar, wadda jaridar New York Times da World Street Journal suka samu ta ce ya kamata Amurka ta yi amfani da karfin soji wajen yakar gwamnatin Bashar Al-Assad, domin a taka mata birki game da yadda take yawan warware yarjejeniyar dakatar da bude-wuta idan an kulla.

Suka ce babu tababa cewa ya dace a dauki matakin kawo karshen yakin basasa a Syria.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ba ta komai a kan wannan takardar da aka tsegunta bayanan da ta kunsa ba.