BH: An kashe mata 18 a wurin zaman makoki

Mayakan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta dade tana kai hari jihar Adamawa

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu mata 18 a wurin wani zaman makoki a kauyen Kuda da ke jihar Adamawa a Najeriya.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce maharan sun shiga yankin ne a kan babura inda suka bude wuta kan mata da kananan yara da suka taru domin zaman makokin wata rasu da aka yi.

Maharan sun kuma kona gidaje da dama a kauyen, wanda ba shi da nisa da dajin Sambisa - maboyar kungiyar ta Boko Haram.

An garzaya da wadanda suka samu raunuka a harin, wanda aka kai da yammacin ranar Juma'a, zuwa asitin da ke kusa da kauyen.

Wani mazaunin wurin Moses Kwagh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har yanzu akwai matan da ba a gansu ba tun bayan kai harin.

A wani lamarin na daban, jami'an tsaro sun ce sun kashe wasu 'yan kunar bakin wake guda biyu da ke dauke da bama-bamai a garin Maiduguri, na jihar Borno.

An kashe mutanen ne a kusa da gidan mataimakin gwamnan jihar.

Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da kungiyar Boko Haram, wacce ta yi mubaya'a ga IS, ta addaba, kafin sojoji su tarwatsa 'ya'yan kungiyar.

Hakan ne ya sa suka tare a dajin na Sambisa mai girman gaske, kuma daga nan ne suke kai yawancin irin wadan nan hare-hare.