Sojojin Iraq sun ƙwace Fallujah

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Dakarun sun mazaya zuwa cikin Fallujah ranar Jumma'a bayan sun kwace iko da yammaci da gabashin birnin

Firayim Ministan Iraki, Haider al Abadi ya sanar da cewa sojojin gwamnati sun kwace iko da birnin Fallujah, bayan sun shafe kusan mako hudu suna ba-ta-kashi da mayakan IS.

Ya dai yi jawabi ne ta gidan Talabijin, amma ya ce har yanzu da sauran rina a kaba, saboda akwai ragowar tsirarun mayakan IS din a birnin, wadanda ya ce za a gana da su nan ba da dadewa ba.

Ya ce mun yi alwashin kwato Fallujah, kuma Allah ya yi. Sojojinmu sun isa Jarumai, sun kutsa birnin Fallujah kuma sun kwace iko da shi. Da sauran mayakan IS, amma da yardar Allah za a yi maganinsu nan da 'yan sa'o'i kadan.

Firayim Ministan ya bayyana cewa abin da sojojin za su sa a gaba shi ne kwace birnin Mosul daga hannun mayakan IS, wato birnin da IS din suka yi kaka-gida, kuma shi ne birnin da ya fi kowanne dadewa a hannunsu.