Babu shugaban da ya lashe kyautar Mo Ibrahim

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kirkiri wannan kyauta a shekarar 2006

Gidauniyar Mo Ibrahim ta sake sanar da cewa babu wani shugaba da ya cancanci samun kyautar dala miliyan biyar a kan bai wa tsohon shugaban kasa a Afirka da ya yi jagoranci mai nagarta.

Tukwicin dai shi ne mafi daraja a duniya, kuma tun lokacin da aka kirkiri wannan kyauta, a shekara ta 2006 sau hudu ne kawai aka samu wadanda suka cancanta.

Mo Ibrahim, wanda shi ne ya kirkiro tukwicin, ya ce a wannan karon ma ba a samu shugaban da ya cika sharudan samun kyautar ba.

Ka'idojin samun wannan lambar yabo sun hadar da samun shugaba wanda ke gudanar da cikakken mulkin dimokradiyya babu magudi, wanda ya kawo ci gaba a kasa ya kuma yi dokokin da za su ka taimakawa talakawa, sannan ya sauka daga kan mulki bayan wa'adinsa ya kare ba tare da ya yi ta-zarce ba.