Za a agazawa Rio de Jeneiro gabanin wasannin Olympics

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Brazil ana saura kasa da kwana 50 a fara gasar wasannin motsa-jiki na duniya, Gwamnan jihar Rio de Jeneiro, Francisco Dornelles ya ce karfin jihar ya gaza, don haka ba ta da kudin da za ta yi dawainiyar jama'a da shi.

Gwamnan ya ce ya sanar da dokar ta-baci ta wannan fuskar ne ko Allah zai sa gwamnatin tarayyar kasar ta agaza musu.

Francisco Dornelles ya yi kukan cewa rashin kudin zai hana jihar tasa tabuka wani abin kirki wajen karbar bakuncin gasar wasannin motsa-jiki, da na nakasssu da zai biyo baya.

Ya ce ala tilas za su dauki wasu matakai na daunin hidima ta fuskar tsaro da sufuri da sauran dawainiyar jama'a, saboda idan ba a yi haka ba, to komai zai lalace.

Sai dai shugaban kasar, Michel Temer ya ce babu abin da zai gagara!

Wakiliyar BBC ta ce asusun gwamnatin jihar na fama da yau-da-gobe, al'amura sai tabarbarewa suke yi, amma a wannan makon shugaban rikon kasar Michel Temer ya yi alkawarin tallafawa da makudan kudade.