Afrika ta kudu: Tukwuici ga matan da suka kare budurcinsu

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar da ke daidaita al'amuran jinsi a Afirka ta kudu ta ce wani tallafin karatun da ake baiwa 'yan matan da suke dauke da budurcinsu a yankin KwaZulu ya saba wa shari'a, kuma ya kamata a dakatar da shi.

Gwamnatin karamar hukumar birni da kewayen Uthukela ce ke ba da tallafin karatun ga Budurwai 16 da suka kai bantensu, domin yin karatu a jami'a.

A bara ne dai aka fara ba da tallafin, wanda ake ce-ce-ku-ce a kansa, wanda aka ce an tsara shi da nufin rage yaduwar cutar SIDA, ko kuma samun ciki a tsakanin 'yan matan da ba su kai munzali ba.

Lardin dai ya fi ko'ina fama da yaduwar cutar SIDA a kasar.