Ana tuhumar 'yan ta'adda uku a Belgium

Hakkin mallakar hoto

Hukumomi a birnin Brussels na kasar Belgium sun ce ana tuhumar 'yan kasar guda uku da aka cafke a wani samamen dare, da laifukan ta'addanci.

An kuma saki mutane tara da aka kama tare da mutanen uku, bayan kasa samun su da laifi da ofishin mai shigar da kara ya yi.

Tun da farkon fari dai an kwashi mutane arba'in don yi musu tambayoyi.

Cikin yankunan da aka gudanar da samamen sun hada ba Molenbeek, a gundumar Brussels da yayi kaurin suna saboda alakarsa da mayaka masu jihadi.

Mutane ukun da ake tuhuma sun hada da Samir C,mai shekaru 27, da Moustapha B,mai shekaru 40, da kuma Jawad B, mai shekaru 29.

Suna fuskantar tuhuma kan aikata laifukan da suka hada da yunkurin kisan kai ta hanyar ta'addanci da kuma shiga kungiyar 'yan ta'adda.

A ranar 22 ga watan Maris ne dai wasu bama-bamai suka hallaka mutae 32 a filin saukar jiragen sama na birnin Brussels.