An yanke wa Morsi hukuncin ɗaurin rai-da-rai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohammed Morsi ya sha musanta zargin da ake yi masa

Wata kotun ƙasar Masar ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan tsohon shugaban ƙasar Mohammed Morsi.

Kotun ta ce ta yanke hukuncin ne kan Morsi da mutum biyu bayan ta same su da laifin yi wa ƙasar Qatar leƙen asiri a lokacin yana kan mulki.

Kazalika, kotun ta yankewa mutum shida, 'yan ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi hukuncin kisa a kan irin wannan laifi.

A baya dai an yanke masa hukuncin kisa da na ɗaurin rai-da-rai.

Tsohon shugaban ƙasar ta Masar yana da damar ɗaukaka ƙara.

An yanke wannan hukunci ne a daidai lokacin da ƙasar ke shan suka daga ƙasashen duniya saboda keta hakkin bil adama.

An hamɓarar da Mohammed Morsi daga kan mulki ne a watan Yunin shekarar 2013 bayan tarzomar da aka yi a kasar.

Shi ne mutumim da ya lashe zaben shugabancin kasar na mulki Dimokradiyya a karon farko tun da aka kawar da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011 sakamakon boren da 'yan kasar suka yi.