Senegal za ta dau matakai kan sare bishiyoyi

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomin Senegal sun ce za su dauki kwararan matakai domin hana sare bishiyoyi ba bisa ka'ida ba a kudancin yankin Casamance.

Ministan tsaro na kasar Augustin Tine yace ya yi amanna za'a kawo karshen dabi'ar nan ba da jimawa ba.

Ya fadi hakan ne a yayin wata ziyartar dazukan dake yankin ne a kusa da iyakar Senegal din da kuma Gambia tare da ministan cikin gida da kuma na muhalli.

A baya ma dai tsohon ministan muhalli na kasar ya bayyana cewa miliyoyin bishiyoyi a fiye da kashi uku bisa hudu na dazukan yankin Casamance sun bace tun daga shekara ta 2010.

Hukumomin sun ce galibin bishiyoyin da ake sarewa ana fasakwaurin su ne ta kasar Gambia makwabciyar Senegal.

Kana ana yin safarar itatuwansu zuwa kasar China inda ake amfani da su domin yin kujeru da gadaje da sauran nau'in ayyukan katako.