An yi musayar Fursunoni a Yemen

Mayakin kabilar Houthi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Yemen ya janyowa 'yan kasar tserewa daga muhallansu.

Bangarorin da ke rikici da juna a kasar Yemen, sun yi musayar fursunoni masu yawa da aka kama watannin da suka gabata a lokacin gwabza fada a tsakiyar birnin Taiz.

An saki kusan 'yan kabilar Houthi 120, inda aka musanya su da mayakan da ke marawa gwamnati baya 74.

Musayar fursunonin dai wani shiri ne da aka yi tsakanin 'yan tawayen, kuma ba ya daga cikin bangaren tattaunawar zaman lafiya da ake yi a kasar Kuwait.

Tattaunawar da aka shafe kusan watanni biyu ana yi, ba tare da an cimma matsaya da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Yemen ba.