'Yan gudun hijirar Falluja na bukatar agaji

Hakkin mallakar hoto

An shiga matsalolin da suka shafi al'umma a kewayen birnin Falluja na kasar Iraqi mai fama da tashin hankali, sakamakon kaurar da fararen hula ke yi.

Ma'aikatan agaji sun ce mutane dubu talatin ne suka tsere daga birnin a cikin 'yan kwanaki kadan da suka gabata, yayinda dakarun gwamanti ke fatattakar mayakan IS daga yankunan birnin.

Yanzu haka dai sansanonin wajen birnin makare suke da 'yan gudun hijira.

A cikin 'yan kwanaki kadan da suka gabata mutane kusan dubu talatin ne suka tsere daga fadan da ake gwabzawa, yayinda dakarun gwamnati suka fatattaki mayakan IS.

Mai magana da yawun hukumar yan gudun hijira ta kasar Norway Karl Schembri, ya shaidawa BBC cewa hukumomin sun shiga matsalolin karancin abinci, da ruwan sha da kuma magunguna.