Ana tuhumar Saraki kan 'dokokin jabu'

Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Saraki ke fuskantar tuhuma

Gwamnatin Nigeria ta ce tana waiwayar batun tsara dokokin jabu da ake zargin majalisar dattawan kasar da yi.

Gwamnatin ta kuma shigar da kara a gaban wata kotu inda take tuhumar shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Sanata Ike Ekweremadu, kan batun sauya dokokin.

Sai dai kuma bangaren sanata Bukola Saraki ya ce abu ne da suka ji shi banbarakwai kuma har yanzu ba a gabatar masa da sammaci ba.

Zuwa yanzu dai kotun ba ta sa ranar da za ta fara sauraren karar ba.

Sharhi, Raliya Zubairu, BBC Hausa Abuja

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ana tuhumar Saraki ne tare da mataimakinsa Ike Ekweremadu

Wata majiya a ma'aikatar shari'a ta Najeriya ta ce gwamnati na kuma tuhumar tsohon akawun majalisar dokokin, Salisu Mai-Kasuwa da mataimakinsa Benedict Efuturi, da hada kai da shugabannin majalisar dattawan wajen tsara dokokin zaman majalisa na bogi.

A bara ne dai 'yan majalisar dattawan suka zabi Bukola Saraki na jam'iyyar APC a matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma Ike Ekweramadu na jam'iyyar adawa ta PDP, a matsayin mataimakinsa.

Wannan zabe da janyo cece kuce a kasar, har ma wasu 'yan majalisar suka kai koke gaban sifeto janar na 'yan sanda, kan cewa an yi zaben ne da dokokin jabu.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da bincike kan lamari, kuma daga bisani ta mika rahotonta ga ministan shari'a na kasar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake zargin Sanata Bukola Saraki da aikata ba daidai ba, inda yanzu haka ana masa shari'a a kotun da'ar ma'aikata bisa tuhumar yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Amma ya sha musanta wannan zargi.