Adadin 'yan gudun hijira ya karu a duniya- MDD

Hukumar lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan adadin mutanen da tashin hankali ya raba da muhallinsu ya kai yawan da ba a taba tsammani ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a karshen shekara ta 2015 mutane sama da miliyan sittin da biyar a fadin duniya sun zama 'yan gudun hijira ko kuma masu neman mafaka, ko kuma mutanen da suka rasa matsugunansu.

Yake-yake da kuma gallazawa sun haddasa karuwar yawan adadin mutanen da ala tilas suka tsere daga gidajensu a bara, wanda ya kawo yawan adadin da MDD ta kididdige zuwa sama da miliyan 65.

Akasarin yan gudun hijrar sun fito ne daga kasashen Syria, da Afghanistan, da kuma Somalia.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole sai gwamnatoci sun bayar da hadin kai game da matsalar, ba wai kawai saboda yan gudun hijirar ba, har ma da daukacin abinda ya shafi al'umma.