'Na so na halaka Donald Trump'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Turereniya lokacin da matashin ya warci bindigar dan sanda

Dan Birtaniyar nan, Michael Sandford, da ake zargi da kwace bindigar wani dan sanda a lokacin gangamin yakin neman zaben Donald Trump a Les Vegas, ya ce ya so ya harbe Donald Trump din ne.

A ranar Asabar ne dai matashin ya je kusa da dan sanda, inda ya fada masa cewa yana son Donald Trump ya ba shi bayaninsa da kansa.

Amma kafin ka ce kwabo sai Michael ya yi wuf ya warce bindigar dan sandan.

Bisa bayanan kotu, Michael Sandford, mai shekara 19, ya ce ya yi takakkiya ne zuwa Les Vegas domin kawai ya aika Trump lahira.

Ya kuma ce ya kwashe kusan shekara guda yana kitsa yadda zai yi ya harbe Mista Trump, yana mai cewa shi ma kuma ya san za a kashe shi.

Har yanzu dai ba a iya tantance dalilinsa na son aikata kisan ba.

Nan ba da jimawa ba ne dai ake sa ran Michael zai bayyana a gaban kotu a Nevada.