Abinda kake bukatar sani game da kuri'ar raba gardama a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Za a gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar Alhamis 23 ga watan Yuni domin yanke shawarar ko Birtaniya za ta fice ko kuma za ta zauna cikin kungiyar Tarayyar Turai wato EU.Menene zaben raba gardama?

Zaben raba gardama wani zabe ne wanda kusan duk wanda ya kai munzalin yin zabe yake iya yi, inda zai nuna ya amince ko kuma bai amince ba game da wata tambaya da aka yi masa.

Ana kuma daukar duk bangaren da ya samu fiye da rabin kuri'ar da aka kada a matsayin wanda ya yi nasara.

Me yasa za a gudanar da zaben raba gardama?

Fira Ministan Biritaniya David Cameron ya yi alkawarin gudanar da kuri'ar idan har ya lashe babban zaben kasar a shekarar 2015.

Kuma ya yi alkawarin ne saboda karuwar kiraye-kirayen da 'yan majalisar dokokin kasar na jam'iyyarsa ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya suke ta yi da kuma 'yan jam'iyyar UKIP.

UKIP na cewa Birtaniyar ba ta da ta cewa tun shekarar 1975, a lokacin da ta kada kuri'ar zama a cikin kungiyar ta EU, a wani zaben raba gardama da aka gudanar.

Suka ce tun daga lokacin ne kuma Tarayyar Turai ta sauya, abin da ya sa ta zama ita ce wuka ita ce kuma nama a rayuwar 'yan kasar ta yau da kullum. ''Don haka lokaci ya yi da 'yan Birtaniya za su samu ta cewa.''

Wacece Kungiyar Tarayyar Turai?

Tarayyar Turai da aka sani da EU kungiya ce da ta kunshi kawancen kasashen nahiyar Turai guda 28 da suke mu'amala ta fuskar tattalin arziki da kuma siyasa.

Kungiyar ta soma aiki ne bayan yakin duniya na biyu domin bunkasa hadin-kai ta fuskar tattalin arziki tare da yadda da cewa kasashen da suka yi huldar kasuwanci tare, za su iya kaucewa yaki da junansu.

Tana da tata takardar kudin wato euro, wacce mambobin kasashe 19 suke amfani da ita, da kuma tata majalisar dokokin, kuma a yanzu kungiyar na shimfida dokoki a fannoni da dama da suka hada da muhalli da sufuri da 'yancin masu sayayya da ma abubuwa kamar yawan kudaden da kamfanonin waya ya kamata su caza

Mecece tambayar da za a yi a zaben raba gardamar?

Shin Biritaniya ta ci gaba da zama mamba a Kungiyar Tarayyar Turai ko kuma ta fice daga Kungiyar?

Su waye za su iya yin zaben?

'Yan Biritaniya da 'yan Ireland da kuma wadanda suka fito daga kasashen da ke cikin kungiyar Commonwealth da suka haura shekaru 18 da haihuwa duka sun cancanta.

Su ma wadanda ke zaune a Birtaniya tare kuma da 'yan Biritaniyan dake zaune a kasashen waje wadanda sunayensu ke cikin rajistar masu zabe a Biritaniyan shekaru 15 da suka gabata duka sun cancanta.

Sai kuma 'yan kasashen da ke cikin kungiyar Tarayar Turai, banda Ireland da Malta da Cyprus - ba za su yi zaben ba.

Su waye suke son Birtaniyan ta fice daga Tarayyar Turai EU?

Jam'iyyar UK Independence UKIP wacce ta samu kusan kuri'u miliyan 4 - wato kashi 13 cikin 100 na wadanda suka yi zabe a babban zaben da aka gudanar cikin watan Mayu, na son ganin Birtaniyan ta fice daga kungiyar.

Haka kuma kusan rabin 'yan majalisar dokokin Birtaniyan da suka fito daga jam'iyya mai mulki ta Conservative, da suka hada da ministoci biyar da kuma 'yan majalisar dokoki 'yan jam'iyyar Labour da na jam'iyyar DUP da yawa suma suna goyan bayan Birtaniyan ta fice.

Mai yasa suke son ganin Birtaniyan ta fice?

Sun yi imanin cewa kungiyar EU ta hana Birtaniyan yin gaba, wanda suka ce kungiyar na tilasta yin amfani da dokoki da yawa a kan kasuwanci.

Sannan kungiyar na cazar kasar biliyoyin fama-famai a duk shekara saboda kasancewarta mamba a cikin kungiyar, ba kuma tare da yi mata wani abin arziki ba.

Suna kuma son ganin Biritaniya ta samu cikakken iko da kan iyakokinta, sannan ta rage yawan mutanen da suke shigowa cikin kasar domin su zauna ko su yi aiki.

Su wa ke son ganin Biritaniyan ta zauna cikin Kungiyar EU?

Firai Minista David Cameron na son ganin Biritaniyan ta zauna cikin kungiyar. Wasu Ministoci 16 a cikin gwamnatinsa su ma na goyan bayan matakin na sa.

Shi ma Shugaban Amurka Barack Obama na goyan bayan Biritaniyan ta zauna cikin kungiyar EU, kamar yadda sauran kasashen Turai irinsu Faransa da Jamus suke son gani.

Mai yasa suke son Birtaniyan ta zauna?

Wadanda suke kamfe din ganin Birtaniyan ta zauna cikin kungiyar EU sun ce kasar na samun babban ci gaba daga kasancewarta mamba - hakan kuma na saukaka mata yin huldar kasuwanci da sauran kasashen Tarayyar Turai.

Sannan sun ce shigowar da 'yan cirani suke yi cikin kasar wadanda mafiyawancinsu matasa ne kuma masu sha'awar yin aiki, na bunkasa tattalin arzikin kasar.

Sun kuma yi imanin cewa matsayin Birtaniyan a idon duniya zai ragu matuka idan ta bar Kungiyar EU.

Suka kara da cewa kasar za ta fi samun kariya idan ta kasance cikin kungiyar kasashe 28 a maimakon tafiya ita kadai.