Darajar Naira ta fadi da kashi 23

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Rahotanni sun ce ba a yi cinki a safiyar Litini ba

Darajar Naira ta fadi da kashi 23 cikin dari a ranar farko ta fara amfani da sabon tsarin musayar kudin kasashen waje, bayan da babban bankin kasar (CBN), ya janye kariyar da ya baiwa Nairar.

Rahotanni sun ce ba a yi ciniki a safiyar ranar Litinin ba amma an ambato manyan dillalai na cewa darajar Naira ta yi kasa da kusan kashi 30 cikin dari idan aka kwatanta da farashin CBN na baya.

Sabon tsarin musayar kudin na da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar wanda ke fuskantar babban kalubalen da bai taba yin irinsa ba a shekaru da dama.

A ranar Litinin ana musayar Naira 255 a kan dala daya a kasuwannin hukuma, yayin da rahotanni ke cewa ta kai 325-345 a kan kowacce dala a kasuwannin bayan fage.

Faduwar farashin mai a duniya ya durkusar da kudin jama'a dalilin da yasa ake fuskantar karancin kudin kasashen waje da za a biya kayayyakin da ake shigowa da su kasar.

Masu kasuwanci da masu zuba jari sun shafe watanni suna kira ga gwamnati ta karya darajar Naira saboda karancin kudin kasashen waje na takure tattalin arzikin kasar.