Buhari ya gargadi Fayose kan matarsa Aisha

Hakkin mallakar hoto twitter
Image caption Mista Fayose ya yi wa matar shugaban Najeriya kage

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da wani 'kage' da gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya yi kan matarsa Aisha Buhari, inda ya danganta ta da wata badakalar cin hanci a Amurka.

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya ce bai kamata a bar Fayose ya dulmiyar da 'yan Najeriya da zantukansa "na karya" ba.

Muna "gargadi da kakkausar murya ga Mista Fayose ya san cewa Aisha Buhari na da damar kare mutuncinta".

Garba Shehu ya kara da cewa ya kamata gwamnan ya shiga "taitayinsa ya san cewa bambancin siyasa ba lasisi ba ne na cin zarafin jama'a".

A ranar Litinin ne gwamna Fayose ya shaida wa kafofin yada labarai cewa Aisha Buhari na da hannu a badakalar cin hanci da ta hada da wani dan majalisar dokokin Amurka William Jefferson, da aka yankewa hukunci a shekarar 2009.

Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta ce, Aisha Buhari ba ta da hannu ko wata alaka da wannan badakala da Fayose ya dangantata da ita.

Gwamna Ayo Fayose na sahun gaba a jerin 'yan adawar da ke sukar manufofin gwamnatin Buhari da kuma jam'iyyar APC mai mulki.