Bemba zai sha daurin shekara 18

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jean Pierre Bemba yayin zaman sauraron kara a kotun ICC

Kotun hukunta masu aikata miyagun laifuka ta duniya ICC, ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban Congo, Jean Pierre Bemba, hukuncin daurin shekara 18 a gidan yari.

A ranar Talata ne kotun ta ICC ta yanke wannan hukunci bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin mutane.

Bemba zai yi shekara goma ne a gidan yarin, ganin cewa ya riga ya shekara takwas a tsare.

Kotun dai ta samu dakarun da Bemba yake marawa baya mai suna Congolese Liberation Army, da laifin kai wa fafaren hula hare-hare, a makwabciyar kasar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.

An ce Mista Bemba ya tura dakarun nasa ne guda 1,000 domin su je su kara da wata kungiyar 'yan tawaye a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya.

An kuma gano cewa dakarun sun yi amfani da karfin tuwo wajen yi wa mata fyade, baya ga hare-haren da suka aiwatar a kan fararen hula.

Mai gabatar da kara na kotun ta ICC dai yana son a yankewa Bemba hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 25.

Har yanzu dai Jean Bemba yana samun goyon baya daga jam'iyyarsa ta MLC, a inda kuma ta yi barazanar daukaka kara.