ICC za ta yanke wa Bemba hukunci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jean Pierre Bemba yayin zaman sauraron kara a kotun ICC

A ranar Talatar nan ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC za ta yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, Jean Pierre Bemba, hukunci, bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin mutane.

Kotun dai ta samu dakarun da Bemba yake marawa baya mai suna Congolese Liberation Army, da laifin kai wa fafaren hula hare-hare, a makwabciyar kasar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.

An ce Mista Bemba ya tura dakarun nasa ne guda 1000 domin su je su kara da wata kungiyar 'yan tawaye a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya.

An kuma gano cewa dakarun sun yi amfani da karfin tuwo wajen yi wa mata fyade, baya ga hare-haren da suk aiwatar a kan fararen hula.

Mai gabatar da kara na kotun ta ICC dai yana son a yankewa Bemba hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 25.

Har yanzu dai Jean Bemba yana samun goyon baya daga jam'iyyarsa ta MLC, a inda kuma ta yi barazanar daukaka kara.