Avengers sun musanta tsagaita wuta

Image caption Niger Delta Avengers ta ce tana fafutika ne domin ganin mazauna yankin sun ci moriyar arzikin da Allah ya yi musu

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Niger Delta Avengers, ta musanta cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce wasu jami'an gwamnatin kasar sun shaida masa cewar 'yan bindigar sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a makon da ya gabata.

Jami'an sun ce kungiyar Avengers ta amince da hakan ne bayan tattaunawarsu da ministan mai da kungiyoyin al'ummomi da kuma gwamnonin yankin.

Amma a shafinta na Twitter, kungiyar ta rubuta cewa, ''NDA ba za ta iya tuna wata yarjejeniya da ta cimma da gwamnatin Najeriya ba.''

''Yana da matukar wahala shawo kan NDA su shiga tattaunawar amma mun san samu mun yi hakan ta hanyar amfani da wasu hanyoyi domin cimma wannan zaman lafiya," kamar yadda wani jami'i ya shaida wa Reuters.

Wasu daga cikin jaridun Najeriya ma sun rawaito wannan labari.

Kungiyar ta Niger Delta Avengers dai ta dauki alhakin fasa bututan man fetur da dama, ciki har da na kamfanin Shell da Chevron.

Sau da dama kungiyar tana shan alwashin durkusar da harkokin man fetur na kasar.

Kwanakin baya 'yan kungiyar suka ce za su yi sulhu da gwamnatin kasar, inda suka nada wasu manyan mutanen yankin na Naijda Delta domin shiga tsakaninsu da gwamnatin.

NDA ta ce tana fafutika ne domin ganin an samu 'yanci a yankin na Naija Delta, wanda ta ce mazauna yankin ba sa cin moriyar arzikin man da Allah ya yi musu.