Nigeria ta sallami likitocin da ke yajin aiki

Wata likita a Nigeria
Bayanan hoto,

Matakin ka iya kara jefa harkokin lafiya cikin rudani

Gwamnatin Najeriya ta sallami likitocin da ke samun horo na kwarewa a asbitocin gwamnatin tarayya wato (resident doctors).

Ministan kiwon lafiya na kasar Isaac Adewole ya ce daina zuwa aiki da wasu daga cikin likitocin suka yi ya sabawa dokar tsarin aikin gwamnati.

Likitocin, wadanda ke koyon aikin a sassan kasar da dama, na yajin aiki ne dangane da batun albashi.

A wata sanarwa da ministan ya fitar, ya umarci shugabannin cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnatin tarayya su maye gurbin likitocin da ke yajin aiki.

"Abin takaici ne ace likitocin sun bar wuraren aikinsu duk da cewa, ana tattaunawa da wakilan kungiyarsu a kan korafin da suke da shi," a cewar Misata Adewole.

A lokacin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ma likitocin sun yi irin wannan rikici da gwamnati, inda aka bayar da sanarwar sallamarsu gaba daya, amma daga bisani aka dawo da su bakin aiki.

Wadannan likitoci na taka rawa sosai a fannin kiwon lafiya a kasar, kuma masu sharhi na ganin matakin ka iya kara lalata al'amura a fannin lafiyar kasar.

Shugaban Majalisar Wakilan kasar Yakubu Dogara na kokarin shiga tsakanin likitocin da kuma ma'aikatar lafiya domin shawo kan matsalar.