Annan ya soki ICC game da shari'ar Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP

Tsohon babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, ya soki kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, game da yadda ta gudanar da shari'o'in shugabannin kasar Kenya.

Mista Annan ya fadawa jaridar Financial Times cewa, bai kamata ace an bar shugaba Uhuru Kenyatta da kuma mataimakinsa William Ruto sun cigaba da walwalarsu a lokacin da ake musu shari'a ba

Kotun ICC dai ta yi watsi ne da zarge-zargen aikata laifuka kan Bil-Adama da ake yi wa mutanen biyu, amma ta ce an tsoratar da shaidu.

Shari'o'in dai na da alaka da tashin hankalin da ya biyo bayan zabukan shekarar 2007 masu cike da takaddama.

An kashe mutane 1,500 sannan an tilastawa mutane 600,000 barin gidajensu yayin da rikicin kabilanci ya bazu a kewayen kasar.

Dukkanin mutanen biyu dai sun musanta zarge-zargen da ake musu, sannan sun zargi kotun ICC da yi wa shugabannin Afrika bita-da-kulli

Kenya ta ce zata janye daga kotun ICC.