Tarzoma ta barke a Afirka ta kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zargi masu tarzomar da kai wa 'yan sanda hari

'Yan sandan kasar Afirka ta kudu na can suna kokarin kwantar da tarzomar da ta barke a yankuna da dama na Pretoria, babban birnin kasar.

Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin kasar ta yi kira da a zauna lafiya, tana mai cewa wasu masu tarzoma sun far ma 'yan sanda ta hanyar jifan motar da suka ciki da duwatsu.

Kafafen watsa labaran kasar sun nuna hotunan manyan hanyoyin da masu tarzomar suka rurrufe.

Wasu rahotanni sun ce an fara tarzomar ne a yankin Tshwane sakamakon zaben da aka yi wa wani domin tsayawa takarar magajin birnin a karkashin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

Gwamnatin kasar dai ta yi kira a zauna kan tebirin sulhu domin kawo karshen rashin jituwar da ta faru sanadin zaben mutumin.