'Bauchi ta gaza tantance ma'aikatan-bogi'

A Najeriya, gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin kasar ya amsa cewa gwamnatinsa ta gaza samun nasara a aikin da ta sanya a gaba na tantance ma'aikata da masu karbar kudin fansho da nufin gano na-bogi.

Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a birnin Bauchi, inda ya ce aikin ya ci-tura ne saboda an samu kura-kurai na ajizanci da kuma na ganganci.

Gwamnan ya fara da shaida wa wakilinmu, Is'haq Khalid, dalilansa na rashin gamsuwa da aikin tantance ma'aikatan:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsin tattalin arziki da ya rage kudin shiga da jihohi ke samu ya sa jihohi da dama sun kaddamar da aikin tantance ma'aikata domin gano na-bogi.

Wannan lamari dai ya jefa ma'aikatan jihohi da dama cikin garari.