Niger: An kai hare-hare wasu kauyuka biyu

Hakkin mallakar hoto none

Hukumomi a Jamhuriyar Niger sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kai hare hare a Kauyuka biyu dake yankin Diffa inda suka kashe limamin garin guda, tare da kwashe kayan abinci.

Harin da ake kayautata zaton cewa 'ya'yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai shi, ya faru ne lokacin da mazaunan kauyukan biyu Booro da Arikoukouri ke sallar magaruba bayan sun kai azumin su.

Garuruwan Boori da Arikoukouri na cikin wani yanki ne mai wahalar shiga ga kungiyoyin agaji bisa dalilai na karanci , koma rishin jama’an tsaro .

Kungiyar Boko Haram na cigaba da kai hare harenta a jamhuriyar Niger.