Congo: Katumbi zai sha daurin shekara 3

Hakkin mallakar hoto
Image caption Katumbi na gaba-gaba a 'yan takarar Shugabancin Kasar

Wata kotu a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta yankewa jagoran 'yan adawar kasar Moise Katumbi hukuncin zaman gidan yari na shekara uku game da wata takaddama da ta shafi sayar da wani gida.

Hukuncin zai hana Mista Katumbi, wanda ake ganin shine na gaba-gaba a masu neman kujerar shugabancin kasar, tsayawa takara a zabukan da za a yi cikin watan Nuwamba.

Mista Katumbi dai ya bar Congo ne a watan da ya gabata bayan da aka zarge shi da daukar sojojin haya na kasashen waje a yunkurin da ake zargin yana yi na hanbarar da gwamnati -- zarge-zargen da ya musanta.

Tsarin mulkin kasar ya haramtawa shugaban kasar mai ci, Joseph Kabila, daga tsayawa takarar wa'adin mulki na uku, amma masu suka sun zarge shi da kokarin makalkalewa a kan mulki.