Tsawa ta kashe mutum 79 a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutum 53 ne suka mutu a jihar Bihar

Jami'ai a Indiya sun ce akalla mutum 79 ne suka mutum bayan tsawa ta fada musu a jihohin Bihar da Jharkhand da kuma Madhya Pradesh.

Mutum 53 ne suka mutu a jihar Bihar, yayin da mutum 10 suka mutu a a gabashin Jharkhand, sannan mutum 16 suka mutu a Madhya Pradesh.

Rahotanni sun ce akasarin mutanen sun mutu ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu, yayin da ake tafka ruwan sama.

Ana yawan yin tsawa a India lokacin da ake tafka ruwan sama.

Alkaluma sun nuna cewa akalla mutum 2,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon fadawar da tsawa ta yi musu a India tun daga shekarar 2005.