Boko Haram: ''Yunwa ta kashe mutum 200''.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mafi yawan yara a sansanon 'yan gudun hijra na fama da karancin abinci mai gina jiki

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya Medicins San Frontier, MSF ta ce kusan mutum dari biyu ne -- wadanda suka tserewa rikicin Boko Haram -- suka mutu saboda matsananciyar yunwa da kishirwa a watan da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce akwai bukatar agajin gaggawa a sansanin 'yan gudun hijra da ke Bama, wanda yanzu haka yake dauke da 'yan gudun hijra fiye da dubu ashirin.

Kungiyar ta kara da cewa mafi akasarin 'yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin yanayi, kuma yawancin su yara ne wadanda da an duba lafiyarsu za a ga cewa suna fama da rashin abinci mai gina jiki.

Wata kididdiga da majalisar dinkin duniya ta yi ta nuna cewa fadan da ake yi tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da kuma sojojin Najeriya ya tilasta wa mutane kusan miliyan biyu barin gidajensu.

MSF ta ce mazauna sansanin da dama na cikin matukar kaduwa kuma yaro daya cikin biyar na fama da cutar tamowa.

A cewarta, mutanen da suka rasa matsugunansu a Bama sun ce ana binne mutum kusan 30 a kullum wadanda suka mutu sanadiyar yunwa ko cuta.

Kungiyar ta kara da cewa ko da ya ke abu ne mai matukar hadari a yi tafiya ta kan hanyoyin yankin, amma jami'anta sun je Bama ranar Talata.

Ta ce hakan ya faru ne bayan sun samu rakiyar dakarun sojojin Najeriya.