EFCC ta kama Ɗakingari

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nigeria EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Usman Dakingari.

EFCC ta kama tsohon gwamnan ne bisa zargin karkatar da wasu kudade da suka kai naira Biliyan daya zuwa jam'iyyar PDP domin yakin neman zabe.

Sanarwar da Kakakin ofishin hukumar a shiyyar arewa maso yamma da ke Kano, Medard Ehimika ya aike wa BBC ta ce, ana tsare da tsohon gwamnan inda ake masa tambayoyi.

Gwamnan yana fuskantar tambayoyin ne a kan rawar da ya taka wajen rabon kudin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP da ya kai Naira Miliyan 450.

Sannan kuma ana neman ya yi karin bayani kan yadda aka karkatar da wasu naira miliyan 550 daga asusun jihar Kebbi zuwa jam'iyyar PDP a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a bara.

Sanarwar ta ce, tsohon gwmanan wanda yanzu haka yake tsare a ofishin EFCC a Kano yana ba da hadin kai a binciken da ake yi masa.