An kori hafsoshin soja biyu a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamadou Issoufou

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun kori wasu hafsoshin soja guda biyu.

Ana zargin su ne dai da aikata mumunan laifi a cikin aikinsu.

Hafsoshin sojan na daga cikin sojojin da gwamnatin ta Nijar ke tsare da su tun cikin watan Disamba na 2015.

Gwamnatin na zarginsu ne da yin wani yunkuri na kifar da gwamnatin Mahamadou Issoufou.