An sace ma'aikatan kasashen waje a Nigeria

Image caption Ana yawan sace mutane domin karbar kudin fansa a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace ma'aikatan kamfanonin kasashen waje bakwai a birnin Calabar da ke kudancin kasar.

Uku daga cikin su dai 'yan kasar Australia ne, biyu 'yan Najeriya, daya dan kasar New Zealand ne, sai kuma dan Afirka ta kudu.

Rahotannin sun kara da cewa 'yan bindiga kimanin 30 sun yi wa mutanen kwanton-bauna ne a lokacin da suke tafiya a motarsu ranar Laraba da safe.

Sun kara da cewa an kashe direban motar sannan aka yi awon-gaba da ma'aikatan na kamfanin Macmahon.

Firai Ministan Australia Malcolm Turnbull ya ce har yanzu ba a san 'yan bindigar da suka sace 'yan kasar tasa ba.

Mr Turnbull ya kara da cewa, "Wannan babban al'amari ne, kuma babban laifi. An kashe mutum daya, sannan aka sace mutum bakwai."

Ana samun rahotanni masu cin karo da juna kan yawan mutanen da aka sace.

Sai dai kwamishinan 'yan sanda Jimoh Ozi-Obeh ya shaida wa manema labarai cewa suna yin aiki tare da sojojin ruwa domin ganin cewa an sako dukkan mutanen ba tare da ko da kwarzane ba.