Tallafin noman shinkafa bai rage tsada ba

Hakkin mallakar hoto SKAZNOV
Image caption Gonar shinkafa

A Najeriya domin wadatar da kasar da shinkafar da kuma rage shigowa da ita daga waje, shugaban kasar ya kaddamar da shirin tallafawa manoman shinkafa na kasar.

Ana sa ran hakan zai taimaka wajen bunkasa yawan shinkafar da ake samarwa.

To sai dai ga dukan alamu hakan bai taimaka ba wajen sauko da farashin shinkafar ba.

A watan Nuwamban bara ne shugaban Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin na bayar da bashi naira biliyan 20 ga manoman shinkafa da alkama a jihohi 14 na kasar a Birnin-kebbi babban birnin jihar Kebbi.