Kai-tsaye: Biritaniya ta fita daga Tarayyar Turai

Latsa nan domin sabuntawaMun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kan fitar Biritaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.Ku kasance da shafin BBCHausa.com domin samun cikakkun bayanai kan wannan labari da ma sauran labarai daga sassan duniya daban-daban.

14:03 Shugabar Asusun bayar da lamuni na duniya Christine Lagarde ta ce, "Mun ga hukuncin da al'umar Biritaniya suka yanke. Muna kira ga hukumomi a kasar da ma kasashen Turai su hada kai domin yin aiki wajen ganin sun kafa sabuwar dangantaka ta fuskar tattalin arziki tsakanin Biritaniya da Tarayyar Turai, ciki har da sharuda da ka'idojin yin dangantakar."

Hakkin mallakar hoto

13:49 Wata 'yar majalisar dokokin jam'iyyar Labour, Margaret Hodgeta ta gabatarwa 'yan jam'iyyar tasu wata wasika ta kuri'ar nuna rashin goyon baya ga shugaban jam'iyyar Jeremy Corbyn, kuma Ann Coffey wata 'yar majalisa ta goyi bayan hakan.

12:27 Dan majalissar dokokin Birtaniyar na jam'iyyar Labour, Chris Leslie ya ce "Ya kamata na yi nazari a kan makomata na kuma yanke shawara a kan ko zan ajiye mukamina".

12:40<span >A wani mataki da ake gani martanin Amurka ne na farko tunda Biritaniya ta zabi ficewa daga Tarayyar Turai, mataimakin shugaban kasar Joe Biden ya ce "mun so sakamakon zaben raba-gardamar ya zama ba wannan ba."

12:25 Shafin matambayi ba ya bata, Google, ya ce an samu karuwar mutanen da ke neman takardar zaman Ireland bayan 'yan Biritaniya sun zabi ficewa daga Tarayyar Turai.

Hakkin mallakar hoto Reuters

12:21 Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce dole mu "nutsu" bayan Biritaniya ta zabi ficewar daga Tarayyar Turai. A wani jawabi da ta yi a birnin Berlin, Angela Merkel ta kara da cewa: "Tarayyar Turai da jama'arta suna da ra'ayoyin da suka sha bamban. Don haka dole Tarayyar ta Turai ta nuna wa jama'ar da ke cikin ta hanyoyin da take bi domin ci gaban rayuwarsu".

11:48 Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya shaida wa wani taron manema labarai a Brussels cewa: "Muna fatan Biritaniya za ta kasance aminiyar Tarayyar Turai a nan gaba."

11:25 Tsohon magajin birnin London, wanda ya yi fafutikar ganin Biritaniya ta fita daga Tarayyar Turai, Boris Johnson, ya ce 'yan kasar "sun yanke hukuncin sake jan ragamar kasarsu" bayan da suka zabi ficewa daga Tarayyar.

Ya kara da cewa masu zabe "sun binciki zuciyarsu inda suka ba ta amsa mai gamsarwa."

11:11 Firai Ministan Biritaniya David Cameron yana fadar Buckingham Palace inda yake ganawa da Sarauniyar Ingila bayan 'yan kasar sun kada kuri'ar amincewa su fice daga kungiyar Tarayyar Turai.

10:48 Kamfanin IAG, wanda ya mallaki jiragen saman British Airways, ya yi amannar cewar fitar Biritaniya daga Tarayyar Turai ba za ta yi mummuna tasiri a harkokin kasuwancinsa ba. Ko da ya ke ya ce gabanin zaben raba-gardamar, kamfanin ya samu dan koma-bayan kasuwanci, amma yanzu yana sa ran samun gagarumar riba.

10:40 Tsohon Firai Ministan Biritaniya, Tony Blair, ya shaida wa gidan talabijin na Sky News cewa ficewar kasar daga Tarayyar Turai zai haifar da babbar illa ga kasar. A cewarsa, sakamakon zaben abin "matukar bakin ciki ne ga kasar nan, da Turai da ma duniya baki daya".

10:22 Darajar hannun jari a bankin Barclays sun fadi da kashi 24 cikin 100 - bayan da tafi da kusan kashi 30 a farkon bude kasuwar shunkun kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP

10:09 Mutumin da ake sa ran zai yi wa jam'iyyar Republican takarar shugabancin Amurka Donald Trump ya ce "abu ne mai kyau" da al'umar Biritaniya suka "kwato kasarsu", bayan da suka zabi ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

10:00 Magajin birnin London, Sadiq Khan, ya tabbatar wa 'yan Biritaniya da ma masu zuba jari daga kasashen waje cewa birnin zai ci gaba da zama cibiyar kasuwanci

09:50 Firai Ministan Ukraine Volodymyr Groysman ya ce "yau wata rana ce maras dadi ga kungiyar kasashen Turai. Sai dai na yi amannar cewa kasashen Turai za su ci gaba da hada kansu, saboda burinsu na mulkin dimokradiyya iri daya ne".

09:45 Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato babban bankin Switzerland yana cewa tun da farko ya dauki matakin kare darajar kudin kasar, wato Swiss franc, wanda ake dauka a matsayin tudun-mun-tsira a tsakanin kudaden duniya, a kasuwar musayar kudaden waje dangane da tasirin ficewar Biritaniya daga Tarayyar Turai.

09:28 Shugaban Babban Bankin Ingila, Mark Carney, ya ce za a fuskanci rashin tabbas a harkokin kasuwancin Biritaniya, yana mai cewa "amma tuni muka shiryawa hakan."

Hakkin mallakar hoto PA

09:00 Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya ce ya dole ne a yi dukkan abin da ya kamata domin kare ayyuka da kuma dokokin su a Biritaniya.

08:53 Ministan harkokin kasashen waje na Jamus Frank Walter Steinmeier ya bayyana fitar Biritaniya daga Tarayyar Turai da cewa "rana ce ta bakin ciki ga kasashen Turai da kuma ita kan ta Biritaniya".

08:41 Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Firai Ministan Biritaniya ta ce David Cameron zai sauka daga kan mulki a watan Oktoba bayan 'yan kasar sun zabi ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP

08:35 Shugaban jam'iyyar UKIP Nigel Farage - wanda ya kwashe shekara 20 yana fafutikar ganin Biritaniya ta fita daga Tarayyar Turai - ya ce sakamakon zaben tamkar ranar 'yanci ce ga 'yan kasar:

08:29 Masu son ficewa sun kai kashi 52 cikin 100, kuma yawancin su sun fito ne daga Ingila da Wales, yayin da wadanda suka zabi kin ficewa suka kai kashi 48, akasarin su na zaune a London, Scotland da Arewacin Ireland.

08:19 Da asubahin nan ne sakamakon zaben raba-gardamar ya fara bayyana, inda ya nuna cewa masu son Biritaniya ta fice daga Tarayyar Turai sun yi nasara.

08:14 Bayani kai-tsaye kan amincewar da al'ummar Biritaniya suka yi ta fice daga Tarayyar Turai, lamarin da ya kawo karshen sama da shekara 40 da kasar ta shafe a kungiyar.