Dangote zai bude matatun mai a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alhaji Dangote ya ce matatar man za ta fara aiki ne a farkon 2019

Shahararren attajirin nan na Afirka, Aliko Dangote, na shirin kaddamar da matatar man fetur da ba ta gwamnati ba a karon farko a Nigeria.

Alhaji Dangote ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa matatar man, wadda zai kashe $12bn wajen gina ta, za ta fara aiki ne a farkon shekarar 2019.

Reuters ya kara da cewa Alhaji Aliko Dangote yana kuma shirin samar da bututan iskar gas a yankin Afrika ta yamma.

Ya kuma shaida musu cewar yana shirin kaddamar da wani sabon kamfanin siminti a kasashe takwas, wanda hakan zai ninka kasuwanci simintin da yake yi a yanzu.