David Cameron zai sauka daga mulki

Ina ganin bai dace na ci gaba da shugabancin kasar nan ba bayan abin da ya faru."

Firai Ministan Biritaniya David Cameron
AFP

Firai Ministan Biritaniya David Cameron ya bayyana cewa zai sauka daga mulki a watan Oktoba.

Mista Cameron ya dauki matakin ne bayan zaben da 'yan kasar suka yi na ficewa dga kungiyar Tarayyar Turai.

A cewarsa, "bai dace na ci gaba da shugabancin Biritaniya ba tunda 'yan kasar sun dauka matsayin da ya yi hannun-riga da manufofina."

David Cameron ya yi fafutikar ganin kasar ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar ta Tarayyar Turai, yana mai gargadin 'yan kasar cewa duk wani abu sabanin hakan zai jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.

Sai dai duk da haka 'yan kasar ta Biritaniya kashi 52 sun zabi ficewa daga Tarayyar Turai, yayin da kashi 48 suka zabi ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar.