Kaduna: Za a hukunta masu aikata fyade

Hakkin mallakar hoto kaduna govt

Gwamnatin jahar Kaduna a Najeriya, ta nuna matukar damuwa a bisa yawaitar fyade a jahar.

A wani taron manema labarai na musamman da ta kira,gwamnatin na cewa daga yanzu za ta sanya idanu a bisa dukkan wani batu da ya shafi fyade,haka kuma ta bukaci dukkan wani a jahar da ya san da wani batu na fyade da aka lullube da ya sanar da gwamnati don daukar mataki.

Gwamnatin jahar dai na cewa ba zata sake zura ido ana cin zarafin yara kanana ba.

Dan haka duk wanda aka kama ya aikata wannan laifi, to ko shakka ba bu za a hukunta shi kamar dai yadda doka ta tanada.

Ko a makon da ya gabata dai sai da aka cafke wani dan shekaru 67 da zargin yiwa wata yarinya yar shekaru 6 fyade.