Ana tuna kisan kare dangi a Armenia

Hakkin mallakar hoto epa

Fafaroma Francis na cigaba da ziyarar da ya ke a Armenia inda zai kai ziyara wurin da ake tuna kisan kare dangin da aka yi a kasar.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan ya yi tur da kisan da aka yi wa Armaniyawa a shekarar 1915.

Fafaroman ya bayyana kashe-kashen da akayi a kasar a matsayin wata babbar masifa da aka taba yi a karnin da ya shude.

Fafaroman ya ce abin takaici ne wannan kisan kare dangi domin shi ne na farko kuma mafi muni a ire-iren abubuwan da akayi a wancan karni.