Za a yi taro kan fitar Birtaniya daga EU

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar turai za su tattauna kan yadda Birtaniya zata fice daga kungiyar

Nan gaba kadan Kasashe shida da suka jagoranci kafa kungiyar tarayyar turai za suyi taro a birnin Berlin na Jamus saboda kuri'ar da Birtaniya tayi na ficewa daga kungiyar.

Ana kyautata zaton ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Faransa da Italiya da Belgium da Luxembourg da Netherlands za su tattauna a kan yadda Birtaniya zata fita daga kungiyar da kuma yanayin fitar ta ta.

Shugaban hukumar tarayyar turai Jean-Claude Juncker (yunker) ya ce yana so a fara tattaunawa ba tare da jiran sai wani sabon firaministan Birtaniya ya fara aiki ba.

Kazalika ana kuma kyautata tsammanin ministocin za su duba yiwuwar yadda za su hana sauran kasashen kungiyar bin irin matakin da Birtaniya ta dauka, bayan da wasu jam'iyyu da kuma 'yan kishin kasa a kasashen kungiyar suka yi maraba da matakin ficewar Birtaniyan.