'Yan siyasar Birtaniya sun fada cikin rudani

Rikicin siyasar da ya barke bayan ficewar Birtaniya daga tarayyar turai, ya sa wani jigo a jam'iyyar Labour ya rasa mukaminsa.

Hakan ya sa shugaban jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn ya tunbuke rawanin mai magana da yawunsa akan harkokin waje,Hilary Benn.

An dai bada rahoton cewa Mr Benn ya yi ta zuga 'yan majalisar a karkashin jam'iyyar Labour da su ture Mr Corbyn, idan har ya ki sauka daga mukaminsa sakamakon kuri'ar alawadai da suka yi masa.

Rahotanni sun ce an zargi Mr Corbyn da rashin yin azama a kampe din da akayi na tabbatar da cewa Birtaniya ta cigaba da kasancewa a tarayyar turai.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne, firaminista David Cameron ya sanar da cewa nan bada jimawa zai sauka daga mukaminsa.