Angela Merkel: Kada a matsa wa Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce bai kamata a matsa wa Birtaniya da cewa ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai cikin gaggawa ba.

Haka kuma ta ce bai kamata a ba batun hana wasu kasashe ficewa daga kungiyar fifiko ba.

Kasashen da suka kafa kungiyar Tarayyar Turai dai sun bayyana bukatarsu na Birtaniya ta yi hanzarin ficewa daga kungiyar.

Amma Angela Merkel ta ce duk da cewa bai kamata a dauki tsawon lokaci wajen gudanar da tsarin ficewar Biritaniyar ba, ba amfani yin hargowa kan batun.

Ta ce: "A gaskiya, bai kamata tsarin ficewar Birtaniyar ya dauki dogon lokaci ba. Hakan nada muhimmanci, amma ba zan yi wani fada a kan cewa ayi shi cikin gajeren lokaci ba."

A wani taron gaggawa da ministocin kasashen Tarayyar Turan suka yi ranar Asabar a Berlin, sun tattauna akan kuri'ar da 'yan Biritaniya suka kada kuri'ar ficewa daga kungiyar.

Ministan harkokin kasashen waje na Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya yi kira ga Biritaniya da ta yi sauri ta fita, domin kungiyar ta fuskanci harkokin dake gabanta.

Ya ce duk da cewa Tarayyar Turan tana mutunta shawarar da Birtaniyar ta zartar na ficewa daga cikinta, hakkin Turan ne ta maida hankalinta wajen lura da harkokin kungiyar, malmakon bata lokacin kan Biritaniyar.

Kasashe shidda -- wadanda sune tushen kafa kungiyar kimanin shekaru 60 da suka gabata -- sune suka yi taron gaggawar a Berlin.

Kasashen kuwa sune Jamus da Faransa da Italiya da Belgium da Luxembourg da kuma Netherlands.

Birtaniya, wadda ta kada kuri'ar shiga kungiyar a shekarar 1975, ta kada kuri'ar ficewa daga cikinta bayan da Firaminista David Cameron ya amince da gudanar da kuri'ar raba gardama a ranar Alhamis.

Mista Cameron ya yi shelar sauka daga mukaminsa bayan ya gaza shawo kan 'yan Biritaniyar su amince da cigaba da kasancewa cikin kungiyar.

Ya ce zai sauka nan da zuwa watan Oktoba domin wanda zai gaje shi ya samu damar aiwatar da tattaunawa da kungiyar Tarayyar Turan akan ficewar Biritaniyan.

Karin bayani