Euro2016: Portugal ta kai wasan dab da na kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Reuters

Portugal da Wales da kuma Poland, sun kai wasan dab da na kusa da karshe, a gasar cin kofin nahiyar turai da ake yi a Faransa a bana.

Portugal ta kai wasan daf da na kusa da karshe ne, bayan da ta ci Croatia daya mai ban haushi, kuma Ricardo Quaresma ne ya ci mata kwallon.

Ita kuwa Poland ta kai wasan zagayen gaban ne, bayan da ta ci Switzerland a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa kunnen doki daya da daya.

Ita ma Wales ta samu damar kai wa wasan zagaye na gaba a gasar, bayan da ta doke Ireland ta Arewa da ci daya mai ban haushi.

A ranar Lahadi za a ci gaba da wasannin zagaye na biyu tsakanin Faransa mai masaukin baki da Ireland.

Sai Jamus da Slovakia da kuma fafatawa tsakanin Hungary da Belgium.