Sudan ta kudu ta soke bikin samun yanci na bana

Shugaba Salva Kirr
Image caption Shugaban Sudan ta kudu, Salva Kiir

Sudan ta kudu ta ce ba za ta gudanar da bikin samun yancin kai na bana ba, saboda matsalar karancin kudi da ta ke fuskanta.

Ministan labarai na kasar, Micheal Makuel Lueth ya ce za a gudanar da bikin cikar kasar shekara biyar da samun yanci kai daga Sudan ba tare da wasu shagulgula ba.

Gwamnatin kasar ta kuma ce ta fasa sayan motocin alfarma ga sabbin ministoci da aka nada.

Tun bayan da ta samu yanci daga Sudan, kasar Sudan ta kudu ta tsunduma a cikin yakin basasa tare kuma da fuskantar koma baya a tattalin arziki.

Haka kuma darajar kudin kasar ta fadi kuma ma'aikatan gwamnati sun ce basa iya biyan bukatunsu na yau da kullum daga albashin da ake biyansu, wanda galibi ba a biya a kan lokaci