Kwamishinan Tarayyar Turai zai yi murabus

Image caption tutuci

Kwamishinan kungiyar Tarayyar Turai a Birtaniya, Lord Hill zai yi murabus daga aikin sa, kwanaki uku bayan da kasar ta kada kuri'ar ficewa daga tarayyar turai.

Yace sam bai ji dadin sakamakon zaben jin ra'ayin jama'a ba, da ya sa Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar tarayar ta turai.

Ya na mai ra'ayin cewa, ba haka ya so dangantaka tsakin Birtaniya da kungiyar ta kasance haka ba.

Lord Hill yace bai amince ba da ya ci gaba da aiki a matsayin Kwamishinan kula da harkokin kudi ba.

Sai dai kuma ya ce zai kara makwanni kafin yin murabus din dan tabbatar da ya cika dukkan sharuddan da ake bukata ga wanda ya yi murabus.