An kai harin kunar bakin wake Lebanon

Wani hari da aka kai Labanun a baya
Image caption Kasar Labanun na fuskantar hare-haren mayakan jihadi.

Rahotanin daga kasar Lebanon na cewa wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari a gabashin kasar.

Wata kafar yada labaran kasar ta rawaito cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu goma sha uku suka jikkata.

'Yan kunar bakin waken sun tashi bama-baman da ke jikinsu a kauyen Qaa da ke kusa da ikar kasar da Syria.

Ana kyautata zaton masu tayar da kayar baya na kungiyar IS ne suka kai harin.