Burutai ya mallaki kadarori a Dubai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dubai shi ne birnin da 'yan Najeriya masu kumbar susa suka fi sayen kadarori a can

Rundunar Sojin Najeriya ta amince da cewa Babban Hafsan sojin kasa na kasar, Lafatanar Janar Yusuf Tukur Burutai ya mallaki kadarori a Dubai.

Hakan ya bayyana ne a wata sanarwa da daraktan Hulda da Jama'a na rundunar sojin kasar na kasar, Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar .

Sanarwar ta karyata wani labarin da ke cewa Janar Buratai din da matansa biyu sun sayi kadarori a birnin Dubai da suka biya a lokaci guda.

''Duk da sun mallaki kadarorin ba a lokaci guda ba ne suka bayi kudinsu, sun yi ta biya ne a hankali tun shekaru uku da suka gabata,'' kamar yadda sanarwar ta yi karin haske kan maganar.

Ta kuma kara da cewa Janar Buratai ya biya kudaden ne daga cikin kudaden ajiyarsa.

Sanarwar ta zama tamkar raddi ne ga kafar yada labarai ta Sahara Reporters ne, wadda ita ce ta fara wallafa labarin.

Rundunar sojin ta kuma ce sanarwar ba komai ba ce face sharri da aka kulla da zummar zubar da mutuncin janar Buratai.

Sai dai wannan batu ya ja hankali 'yan Najeriya sosai musamman a shafukan sada zumunta da muhawara na kasar, kamar su Facebook da Twitter.