'Scotland na iya hana Birtaniya fita daga EU'

Hakkin mallakar hoto PA

Babbar ministar Scotland, Nicola Sturgeon, ta ce majalisar dokokin Scotland za ta iya hana Birtaniya ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

Birtaniya ta kada kuri'ar neman ficewa daga kungiyar, amma yawancin 'yan Scotland sun goyi bayan cigaba da zama a cikinta.

A hirarta da BBC, Misis Sturgeon ta ce ta yi ammanar cewa sai majalisar dokokin Scotland ta amince da kuri'ar ne kafin Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turan.

Ta ce za ta kuma roki 'yan majalisar Scotland din da kada su amince da fitar Birtaniyan.

Misis Sturgeon ta ce tana kokarin kare mutanenta ne daga barnar da fita da Tarayyar Turan za ta yi masu.

Tun da farko dai ta yi barazanar cewa za ta nemi a sake yin kuri'ar raba gardama a Scotland domin ballewa daga Birtaniya -- kuri'ar da Scotland din ta yi ba tare da samun nasara ba kimanin shekaru biyu da suka wuce.

Scotland na daya daga cikin shiyyoyi hudun da Birtaniya ta kunsa -- sauran ukku sune Ingila da Wales da kuma Ireland ta Arewa.