Isra'ila da Turkiyya za su sasanta

Racep Tayyip Erdogan
Image caption Dangantaka tsakanin kasashen ta yi tsami shekarun da suka gabata.

A ranar Litinin ne ake sa ran kasashen Isra'ila da Turkiyya za su tabbatar da yarjejeniyar da za ta kawo karshen zaman doya da manjan da suke yi tun bayan da Sojin ruwan Isra'ila suka hallaka masu fafutuka shida na kasar Turkiyya.

Jami'ai daga kasashen biyu sun ce an cimma yarjejeniya domin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin su.

Dangantaka ta dan farfado tsakanin kasashen biyu bayan tattaunawar da shugaba Racep Tayyip Erdowan da Benjamin Netanyahu suka yi ta wayar tarho a shekarar 2013.

Haka kuma an ci gaba da tattaunawa a watannin da suka gabata lamarin da ya sanya jakadun kasashen da aka janye suka koma bakin aiki.

A shekarun da suka gabata ne dai Sojin ruwan Isra'ila suka far wa jirgin ruwa na dakon kaya mallakin Turkiyya a kan hanyarsa ta kai kayan agaji ga Palasdinawa a zirin-Gaza.