Ba a biya dakarun Tarayyar Afrika alawus ba

An kwashi tsawon watanni shida ba ba tare da biyan dakarun ba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kwashi tsawon watanni shida ba ba tare da biyan dakarun ba

BBC ta gano cewa ba'a biya dakarun sojin Afrika da ke yaki da kungiyar Al-Shabaab a Somalia alawus dinsu ba har na tsawon a kalla watanni shida.

Tarayyar Turai ce ke biyan dakarun tarayyar Afurkan na Amisom, kuma wata majiyar Tarayyar Turan ta fada wa BBC cewa, an rike kudadan alawus dinsu na watanni shidan da suka wuce a kan batutuwan rashin yin gaskiya.

Shugaban Amisom din ya fadawa BBC cewa yanzu an mika takardun bayanan biyan kudadan na baya.

Ya kamata Tarayyar Turai ta biya kowane sojin Amisom sama da dala 1,000.