Ƙarancin wutar lantarki a Ghana

Image caption Shugaban Ghana, John Dramani Mahma

A Ghana, jama'a na cigaba da kokawa dangane da matsalar karancin wutar lantarki da ke kara tabarbarewa, a fadin kasar.

Ko a karshen makon da ya gabata ma akasarin Accra, babban birnin kasar ya kasance babu wutar lantarki.

Sai dai kuma gwamnatin kasar ta alakanta matsalar da hare-haren da ake kaiwa wuraren hakowa da fitar da mai da iskar gas, a Nigeria.

To amma wasu na ganin cewa rashin wutar ba zai rasa nasaba da irin dimbin bashin kudin iskar gas da Najeriya take bin Ghanar ba.

Wasu kuma na danganta al'amarin da matsalar rashawa da cin hanci da ke addabar mafi yawancin kasashen Afirka.

A baya dai kasar ta Ghana ta zamo wata abin gwada misali wajen samun wutar lantarki ba bu kakkautawa, a yankin Afirka ta yamma.