An kwace ikon gwamnatin Buhari — Saraki

Hakkin mallakar hoto NGR
Image caption Saraki ya ce wasu sun kwace ikon jan ragamar gwamnatin Buhari

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, ya ce wasu tsirarun mutane sun kwace ikon tafiyar gwamnati daga hannun shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Mista Saraki ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu, wacce mai magana da yawunsa ya aikewa manema labarai.

Sanata Saraki ya ce, mutanen da suka aikata hakan sun kwace iko ne domin biyan bukatunsu na karan kansu.

Shugaban majalisar ya yi wadannan kalamai ne sakamakon takun sakar da ke faruwa tsakaninsa da bangaren zartarwa, inda yanzu haka kotu ke tuhumarsa da yin dokokin jabu a majalisar.

Sanarwar ta ce, wannan ''bi-ta-da-kulli'' da ake wa majalisar dokokin na nuna irin matsalar da dimokradiyya ke fuskanta, wadda 'yan kasar suka sha wahala wajen ganin tabbatuwarta.

Mista Saraki ya kara da cewa, wannan tuhuma tasu da ake yi a madadin gwamnatin tarayya na nuna cewa wasu kusoshi a gwamnati sun ki su yarda cewa ana gudanar da majalisar ne bisa dokokinta, wadanda kuma da su ne ake amfani wajen warware duk wata matsala da ake fuskanta a majalisar.

Sai dai ya ce a shirye yake ya cigaba da shanye duk wata barazana da ke fuskantarsa da kuma tsayawa kan gaskiya da sauke nauyin al'umma da ke kansa.

Sanata Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon akawun majalisar dokokin kasar Salisu Mai-Kasuwa na fuskantar tuhuma ne kan yin dokokin jabu a majalisar dattawan kasar.